Hadin gwiwa ta zama hanya daya kawai da ake bi don samun zaman lafiya da moriyar juna, a cewar firaministan Sin
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da tsohon sakataren harkokin waje na kasar Amurka Henry Alfred Kissinger a ranar 25 ga wata a nan birnin Beijing. A lokacin ganawar, Mr Li ya bayyana cewa, kamata ya yi bangarori daban daban su yi shawarwari don kara fahimtar juna, da kuma yin hadin gwiwa don samun zaman lafiya da moriyar juna. Kasar Sin in ji shi tana son hada kai tare da kasar Amurka wajen raya sabuwar dangantakar dake tsakaninsu don amfanawa jama'ar kasashen biyu da kuma taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.
A nasa bayanin, Mr Kissinger ya ce, dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin tana da muhimmanci ga zaman lafiya da bunkasuwar dukkan duniya. Don haka, kamata ya yi a tsara shiri na dogon lokaci, da kara yin mu'amala da juna don inganta dangantakarsu yadda ya kamata. (Zainab)