A ranar Lahadi 19 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce, kasashen Sin da Indiya gaba daya a shirye suke na ganin sun ciyar da wani kokari gaba da zai inganta hadin kai a nahiyar Asiya, su kuma zama wani inji na tattalin arziki a duniya.
A ganawarsa da takwaransa na Iniyan Manmohan Singh, Li Keqiang ya ce, kasashen biyu suna da karfi, dabaru da kuma aniyar hada kai tare domin zama wani alama mai haske a hadin kan kasashen dake nahiyar Asiya, kirkiro da wani injin na tattalin arziki a duniya, samar da babban ribar cigaba da kasuwa wajen bukatun kayayyakin nahiyar Asiya da ma duniya, su kuma inginza dabarun Sin da Indiya a kan cigaba na hadin gwiwwa don zaman lafiya da yalwatuwa.
Firaministan kasar Sin a jiya Lahadi ne ya isa birnin New Delhi a zangonsa na farko na ziyarar aikinsa zuwa kasashen waje tun darewarsa wannan kujera watan Maris. Wanda da saukarsa new Delhi ya bayyana cewa, yana son wannan ziyarar a nuna ma duniya cewa, aminci da fahimtar juna a siyasance yana nan a tsakanin kasar Sin da Indiya, hadin kai na ainihi a bayyane yake kuma akwai wassu ra'ayoyi masu yawa fiye da wasu banbance banbance.
A nashi bangaren. Mr. Manmohan Singh ya ce, gwamnatin da al'ummar Indiya sun ji dadin karamar da firaministan Li ya yi masu na mai da kasarsu ta zama zangon farko a ziyararsu ta farko zuwa kasashen waje, ya ce, akwai wadatattun wurare a duniya da za su samar da wadatattun cigaba ga kasashen Indiyan da kuma Sin, kuma su abokan huldan arziki ne ban a hamayya ba.
A cewarsa, hadin kan Sin da Indiya yana da muhimmanci ga zaman lafiyar duniya da cigabanta baki daya, kuma Indiya tana matukar mutunta wannan hadin kai, sannan a shirye take ta kara mu'amala da Sin don daidaita, inganta da kuma hana abkuwar rikici a kan iyakokin kasashensu. (Fatimah)