Inganta mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin kananan hukumomi zai taka muhimmiyar rawa wajen raya dangantaka a tsakanin Sin da Amurka
Ranar 11 ga wata, a nan Beijing, Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya gana da Jerry Brown, gwamnan jihar California ta kasar Amurka, inda ya ce, inganta hadin gwiwa da mu'amala a tsakanin kananan hukumomin kasashen 2 zai taka muhimmiyar rawa da kuma aza harsashi mai kyau a tsakanin al'umma wajen raya dangantaka a tsakanin kasashen 2.
A yayin ganawar, firaministan kasar Sin ya ce, yanzu an shiga wani sabon zamani na bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, ta haka ya kamata kasashen 2 su ci gaba da kokarinsu ba tare da kasala ba wajen kyautata dangantakar abokantaka da hadin gwiwa da kuma huldar da ke tsakanin manyan kasashe irin ta sabon salo a tsakaninsu, bisa ka'idar girmama juna da samun moriyar juna da nasara tare. (Tasallah)