Karamin ministan harkokin waje na kasar Indiya da sauran manyan jami'an kasar ne suka tarbe shi a filin jiragen sama. A jawabinsa bayan saukarsa Mr Li Keqiang ya lura cewa, a matsayin manyan kasashe masu tasowa biyu a duniya, Sin da Indiya suna kiyaye dangantakarsu yadda ya kamata, wanda ya dace da moriyar kasashen biyu, kana zai taimakawa wajen kiyaye zaman lafiya da wadata a nahiyar Asiya har ma a fadin duniya baki daya. Ya ce a don haka, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Indiya, kana ta maida kasar Indiya a matsayin muhimmiyar abokiya a duniya. Li Keqiang ya yi imani da cewa, ziyararsa a wannan karo za ta sa kaimi ga kara yin mu'amala, hadin gwiwa, fahimtar juna da kuma sada zumunta a tsakanin kasashen biyu, kuma hakan zai taimaka wajen inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa da kiyaye zaman lafiya da wadata a tsakaninsu a nan gaba. (Zainab)