in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Li Keqiang ya jaddada cewa, za a inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Indiya
2013-05-20 20:13:33 cri
A ranar 20 ga wata a birnin New Delhi dake kasar Indiya, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Indiya Manmohan Singh, inda Li ya jaddada cewa, kamata ya yi a sa kaimi ga samun ci gaban hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, da kuma inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa da kiyaye zaman lafiya da wadata a tsakaninsu a nan gaba.

Bangarorin biyu sun amince da yin hadin gwiwa kan muhimman ayyuka a fannonin raya yankin sana'o'i, kayayyakin more rayuwa da dai sauransu, kana sun yi kira da a kafa hanyar tattalin arziki a tsakanin Sin, Indiya, Myanmar da kuma Bangladesh don sa kaimi ga hadin gwiwar kasuwanci a tsakanin Sin da Indiya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China