in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban kasar Indiya
2013-05-22 10:45:51 cri

A jiya Talata 21 ga wata a birnin New Delhi fadar gwamnatin kasar Indiya, shugaban kasar Pranab Mukherjee ya gana da firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda ke ziyarar aiki a kasar. Da farko, Li Keqiang ya isar da gaisuwa da kyakkyawar fata daga shugaban kasar Sin Xi Jinping ga Shugaba Pranab Mukherjee.

Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin da Indiya aminan juna da kuma makwabtan juna ne kuma wani babban ci gaba da ya samu a wannan ziyararsa shi ne cimma matsaya daya da shugabannin biyu suka yi game da habaka moriyar bai daya, da sa kaimi ga hadin gwiwa a dukkanin fannoni, da kara samun daidaituwar baki, tare kuma da kawar da bambancin ra'ayi, ta yadda za a amfanawa jama'ar kasashen biyu ta hanyar raya dangantakar dake tsakaninsu.

Li Keqiang ya bayyana cewa, ana bukatar wani yanayin duniya mai zaman lafiya wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Don haka Sin na fatan kara hadin kai da Indiya tare kuma da zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a kan halin zaman lafiya da wadata, ta yadda za su taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da wadata a nahiyar Asiya har ma a dukkanin duniya.

A nashi gefen Shugaba Pranab Mukherjee ya mika gaisuwarsa ga takwaransa na kasar Sin Xi Jinping ta bakin Li Keqiang. Ya ce, Indiya na fatan hadin gwiwa da kasar Sin, da kuma kiyaye dangantakar dake tsakaninsu, tare da kara raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China