in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya jagoranci taron majalisar gudanarwa
2013-03-19 14:41:06 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jagoranci taron sabuwar majalisar gudanarwa karo na farko a ran 18 ga wata, domin bincike kan yadda za a sa kaimi ga yin kwaskwarima kan hukumomin majalisar, da kuma mai da hankali kan yadda za a tabbatar da sauyin ikon gwamnati.

Bisa tsarin yin kwaskwarima kan hukumomin majalisar gudanarwa da sauyin ikon gwamnatin da taro karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12 ya zartas da shi, taron da aka yi a wannan rana ya mai da hankali ne kan yadda za a kafa hukumomin kai tsaye karkashin jagorancin majalisar, bayar da iznin kafa hukumar sa ido kan abinci da magunguna, sabuwar hukumar yada labaru, hukumar jirgin kasa, da kuma sake kafa hukuma mai kula da harkokin teku, da hukumar makamashi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China