in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya kama hanyar zuwa Pakistan daga kasar Indiya
2013-05-22 15:23:29 cri
A safiyar yau Laraba 22 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kammala ziyararsa a kasar Indiya kuma ya tashi zuwa Pakistan domin ci gaba da ziyararsa a kasashe hudu dake Asiya da Turai.

Kasar Indiya ita ce zangon farko a wannan ziyarar da Li Keqiang ke yi tun hawansa a mukamin firaministan kasar Sin. A lokacin ziyararsa a Indiya, Li Keqiang ya gana da shugabannin kasar ciki hadda takwaransa Manmohan Singh inda suka yi shawarwari a tsakaninsu, inda bangarorin biyu suka cimma matsaya daya cewa, ya kamata, kasashen biyu su mai da bunkasuwar juna a matsayin wani kyakkyawar zarafi ga juna.

Moriya bai daya a tsakaninsu ta fi bambancin ra'ayi yawa. Ban da haka kuma, bangarorin biyu sun bayyana fatan kara hadin gwiwa tsakaninsu domin ci gaba da raya dangantakar dake tsakaninsu a cikin sabon yanayi tare kuma da samar da sabon karfi wajen ingiza tattalin arzikin duniya.

Game da wasu matsalolin da suke fuskanta ta fannin harkar kan iyaka, kasashen biyu sun cimma matsaya daya kan ci gaba da sa kaimin yin shawarwari kan batun shatin iyakar kasa, kyautata tsarin daidaita harkokin kan iyaka, sannan a daidaita bambancin ra'ayi yadda ya kamata don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankuna dake iyakar kasashen biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China