Li ya bayyana cewa, yanzu dangantaka tsakanin Sin da Amurka na kasacewa cikin muhimmin mataki, don haka kamata ya yi a sa kaimi ga bunkasa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa, mai cike da girmama juna, bisa matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
A cewar firaminista Li, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da dora muhimmanci kan dangantaka tsakaninta da Amurka, da fatan za a sa kaimi ga raya dangantakar zuwa mataki na gaba, a fannonin hadin gwiwa da juriya, da kuma yin takara mai kyau tsakanin su, a kokarin samar da yanayi mai nagarta.
A nasa bangare, Jacob Lew ya bayyana cewa, Amurka na fatan sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, bisa yin shawarwari a fannin tattalin arziki da manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, da fatan kasahsen 2 za su kara mu'amala da juna, wajen tsara ka'idojin kasashen duniya, tare da karfafa hadin gwiwa kan tinkarar sauyawar yanayi da sauransu.(Fatima)