in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfin yin rikakafi da tinkarar bala'u na kasar Sin ya karu
2013-05-22 15:06:42 cri

Mataimakin ministan harkokin cikin gida na kasar Sin Mr Jiang Li wanda a yanzu haka ke halartar babban taron tinkarar bala'u na duniya karo na 4 a birnin Geneva na kasar Switzerland, ya gabatar da jawabi a ran 21 ga wata, inda ya ce, gwamnatin kasar Sin na nacewa ga matsayin shigo da ayyukan tinkarar bala'u da tinkarar sauyin yanayi a cikin tsarinta na samun bunkasuwa mai dorewa, kuma tana kara sa kaimi ga inganta sassan rage bala'u, ta yadda za a kara karfin yin rigakafi da tinkarar bala'u.

Mr Jiang Li ya yi bayani kan kokarin da Sin ta yi a cikin shekaru biyu da suka gabata daga fannoni biyar. Sannan ya yi bayyani kan yadda aka ba da agaji lokacin da bala'in girgizar kasa mai tsanani ya auku a gundumar Lushan na lardin Sichuan a watan da ya gabata.

Jiang Li ya nuna cewa, bala'u daga Indallahi sun zama kalubale da dukkanin 'yan adam suke tinkarar tare, don haka ne Sin take fata hadin gwiwa da kasa da kasa kan wasu ayyuka, ciki hadda yin rigakafi, tuntubar juna kan wasu bayanai, ba da agaji cikin gaggawa, kimiyya da nazari, fasahohi, ba da horaswa, rage bala'u a fannoni daban-daban da sauransu. Haka kuma Sin ta na fatan ganin MDD ta shigo da aikin tinkarar bala'u cikin ajandar raya kasa da kasa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China