Hukumar binciken girgizar kasa ta kasar Amurka ta tabbatar da cewa, an yi girgizar kasa da karfe 8 a daren ranar 27 ga wata bisa agogon wurin, wadda ke da cibiyarta a yankin teku dake da nisan kilomita 200 a kudu maso yammacin Prince Rupert, kana mafarin girgizar kasa ta kasance kilomita 10 karkashin kasa. Daga bisani an kara samun tsilla-tsillar abkuwar girgizar kasa karo 8, wadanda karfinsu na tsakanin maki 4.8 zuwa 5.8.
A nata bangare, hukumar binciken girgizar kasa ta kasar Canada ta ce karfin girgizar kasar ya kai maki 7.1. Sa'an nan ma'aikata mai kula da muhallin kasar ta sanar da gargadin abkuwar tsunami, wanda ya shafi kusan dukkan yankin gabar teku dake yammacin kasar Canada, yankin da ya taso daga kusa da jihar Alaska ta kasar Amurka dake arewa har zuwa wurin dake dab da jihar Washington ta kasar dake kudu.
Ban da haka kuma, cibiyar ba da gargadin kare kai daga bala'in tsunami a tekun Pasific ta yi kashedi ga tsibiran jihar Hawaii ta kasar Amurka cewa, girgizar kasar ta riga ta haddasa tsunami, wanda a halin yanzu ke tasam ma Hawaii. (Bello Wang)