Gidan talibijin na kasar Iran ya labarta cewa, girgizar kasa ta ruguza kauyuka guda 4 baki daya, tare da lalata wasu kauyuka guda 6. Wani jami'in dake kula da harkokin samar da kayayyakin jin kai na Iran ya ce, bala'in ya katse dukkan hanyoyin sadarwa da na wutar lantarki a yankin. Don haka, ana amfani da rediyo kawai a kokarin tuntubar hukumomin yankin.
Bugu da kari, hanyoyin samar da ruwan sha sun katse sakamakon bala'in, yanzu ana bukatar ruwan sha, burodi, tantuna da dai sauran kayayyakin zaman rayuwa na yau da kullum. Sannan jami'an wurin sun bukaci mazauna wurin da su kwana a waje don magance sake samun rauni sakamakon aukuwar kananan bala'un girgizar kasa masu tsanani. (Sanusi Chen)