An ce, girgizar kasar ta abku ne a yankin duwatsu dake fama da talauci dalilin rashin kayayyakin more rayuwa masu inganci, kuma an lalata hanyoyin mota da na'urorin sadarwa sosai sakamakon bala'in. Dalilin haka, aka kasa kawo taimako cikin sauri domin tsirar da mutane ta yadda za'a rage hasarar rayukan jama'a da dukiyoyinsu. A halin yanzu ana ci gaba da kokarin bada aikin agaji da kididiga kan wannan bala'in .
Labarin abkuwar girgizar kasa ya tada hankalin shugaban kasar Sin, Hu Jintao, dake birnin Vladivostok na kasar Rasha domin halartar taron kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen Asiya da tekun Pacific wato APEC. Shugaba Hu Jintao ya ba da umarni nan take, inda ya bukaci bangarorin da lamarin ya shafa da su yi kokarin ba da agaji, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi na jama'ar da wannan bala'i ya rutsa da su. A nasa bangare, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao, ya tashi zuwa gundumar Yiliang ba tare da bata lokaci ba, inda ya bada jagoranci ga aikin agaji da ceton jama'a. Sa'an nan gwamnatin lardin Yunnan ita ma ta kaddamar da shirin ko ta kwana na tinkarar bala'in da ya shafi yankin karkara, kana ta tura kungiyar jami'ai zuwa yankin da bala'in ya shafa don kula da aikin agaji.
Ban da haka kuma, kakakin babban magatakardan MDD, Martin Nesirky, ya furta a ranar 7 ga wata cewa, majalisar tana sa ido sosai kan bala'in girgizar kasa da ya abku a gundumar Yiliang dake lardin Yunnan na kasar Sin, kana ofis mai kula da aikin jin kai na MDD na mai da hankali kan yanayin da ake ciki bayan abkuwar bala'in, kuma a shirye yake domin ba da taimako ga gwamnatin kasar Sin. (Bello Wang)