Ranar Laraba 12 ga wata a birnin Nairobi, jami'in hukumar riga kafin abkuwar bala'u ta MDD mai kula da harkokin Afrika ya ce, kasashen Afrika sun fi fama da talauci, saboda haka, basu da karfin magance bala'u.
Wannan jami'i ya nuna cewa, ya zuwa yanzu a nahiyar Afrika, wasu kasashen dake gabashin Afrika ciki har da Somaliya, Habasha da sauransu da kuma yankin Sahel dake arewa maso yammacin Afrika da dai sauran yankuna su kan yi fama da fari, amma an fi fama da bala'in ambaliyar ruwa a wuraren da kogin Zambezi da na Senegal ke malala.(Amina)