Valerie Amos wadda a yanzu haka take ziyara a nan birnin Beijing ta ce, kamata ya yi kasashen duniya su koyi kwarewar kasar Sin a fannonin da suka shafi rigakafi gami da yaki da bala'u, da kafa tsarin tinkarar bala'un da sauransu.
Madam Amos ta ce, akwai matsaloli da dama wadanda suka kunno kai cikin ayyukan ceto bayan abkuwar bala'in girgizar kasa a kasar Haiti a shekarar da ta gabata da kasar Pakistan a wannan shekara, alal misali, yaya ma'aikatan ceto za su yi don neman mutanen da bala'in ya ritsa da su, kuma yaya za'a gudanar da ayyukan ceto yadda ya kamata da makamantansu.
Madam Amos ta kara da cewa, bayan abkuwar matsalar hada-hadar kudi a duniya, kasa da kasa na kara mayar da hankali kan yadda ake amfani da kudi da kayayyakin da suka bayar kyauta, lamarin da ya sa aka fara kawo sauye-sauye ga ofishin daidaita harkokin jin-kai na MDD dake karkashin jagorancinta. An ce, wadannan sauye-sauye za su kyautata aikin rarraba ma'aikatan ceto na majalisar, da kara samar da taimako ga mutanen dake da bukata.(Murtala)