in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutane da suka mutu a sakamakon girgizar kasa a lardin Yunnan na kasar Sin ya karu zuwa 50
2012-09-07 20:34:19 cri
Bisa labarin da hukumar kula da harkokin jama'ar lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa karfe 5 da rabi na yammacin yau Jumma'a 7 ga wata bisa agogon wurin, yawan mutane da suka mutu a sakamakon girgizar kasa da ta abku a gundumar Yiliang ya kai 50, kana mutane fiye da 150 sun ji rauni.

A wannan rana da yamma, hukumar kula da harkokin jama'ar jihar Yunnan ta kara baiwa yanki mai fama da bala'in girgizar kasar gadaje 2000.

Bisa labarin da kamfanin samar da wutar lantarki na jihar Yunnan ya bayar, an ce, ba a samu tasiri ba ga samar da wutar lantarki ga manyan ayyukan da ake gudanarwa a yankin. Kamfanin yana yin jigilar na'urorin wutar lantarki zuwa yanki mai fama da bala'in, da gyara wayar wutar lantarki da suka lalace sanadiyar bala'in, da yin mu'amala tare da hukumomin kula da girgizar kasa da yanayi da sufuri don magance sake lalata wayar wutar lantarki bayan da girgizar kasar ta abku.

Shugaban hukumar kula da girgizar kasa ta jihar Yunnan, Huangpu Gang ya bayyana cewa, yanzu masana suna sa ido kan halin da yankin da girgizar kasar ta abku, kana masanan da hukumar kula da girgizar kasa ta kasar Sin ta tura zuwa yankin suna kan hanyar isa wajen. Don haka ya yi kashedi cewa, domin ba a dade da samun girgizar kasa ba, kamata ya yi a lura sosai kan tartsatsin girgizar kasa, kuma mutane dake yankin da bala'in ya abku, su kiyaye kada su je kusa da duwatsu, don magance abkuwar sauran bala'u a yankin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China