Mataimakin darektan kwamitin daidaita bala'u na kasar Sin kuma ministan harkokin jama'a na kasar Li Liguo ya yi jawabi a gun bikin bude taro cewa, kasar Sin ta samar da agajin aninci da yawansu ya kai kudin Sin RMB miliyan 533 da dubu 200 ga kasashen Afrika cikin gaggawa domin tinkarar fari mai tsanani da ake fama da shi a wasu kasashen Afrika. Ban da haka kuma, gwamnatin kasar Sin da ofishin sakatarorin daidaita bala'u na MDD sun kafa cibiyar tinkarar bala'in fari domin tsara fasalin ba da taimako ga kasashen Afrika dake fama da fari.
Bugu da kari, wakiliyar asusun yara na MDD dake kasar Sin Gillian Mellsop ta nuna godiya ga kasar Sin bisa taimakon abinci da ta samar wa kasashen Afrika, tana fatan kasar Sin za ta gabatar da sakamakon tinkarar bala'in fari ga kasashen Afrika domin ba da gundummawa wajen tabbatar da zaman jituwa a duniya.(Lami)