Bisa labarin da aka bayar, an ce, yawancin matattun an same su ne a yankunan karkara. Wannan bala'in girgizar kasa ya ruguza kauyuka kimanin 60 na yankin.
Kana kungiyar jin kai ta Crescent da Red Cross ta Iran ta bayyana cewa, yanzu ta mayar da wani dakin wasannin motsa jiki a matsayin dakin samar da kayayyakin jin kai, inda ta riga ta karbi mutanen da wannan bala'i ya nutsa da su kimanin dubu 16, kuma ta samar da tantuna dubu 3 tare da sauran dimbin kayayyakin jin kai.
Bayan aukuwar bala'in, shugaba Ahmedinejad na kasar Iran ya fitar da wata sanarwa, inda ya nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamakon bala'in, kuma ya nuna jejeto ga wadanda suke fama da bala'in, kana ya bukaci hukumomin gwamnatin kasarsa da su yi namijin kokari na tallafawa wadanda suke fama da bala'in. (Sanusi Chen)