in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya nuna damuwa sosai kan girgizar kasa da aka samu har sau biyu a kasar Iran
2012-08-13 10:26:01 cri
Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon ya bayyana damuwarsa sosai a ranar Lahadi kan girgizar kasa da aka samu har sau biyu a kasar Iran a ranar Asabar a arewa maso yammacin kasar da suka haddasa mutuwar daruruwan mutane da asarar dukiyoyi.

"Sakatare janar ya kadu sosai game da asarar rayukan daruruwan mutane, da yawan mutanen da suka raunana da rushewar gidaje da aka samu a kasar Iran sakamakon girgizar kasa da ta faru har sau biyu a yankunan birnin Tabriz a ranar 11 ga watan Augusta," in ji kakakin mista Ban Ki-moon a cikin wata sanarwa.

Mista na isar da sakon ta'azziya ga gwamnati da kuma al'ummar kasar Iran musammun ga iyalan da wadannan bala'u suka rutsa da 'yan uwansu, in ji wannan sanarwa.

Adadin mutanen da suka mutu a cikin wadannan zirgizar kasa biyu ya cimma 300, a cewar kamfanin dillancin labarai na kasar Iran Fars, da ya rawaito kalaman wani jami'in dake wurin.

Girgizar kasa mai karfi 6,2 bisa ma'aunin Richter ta abku bisa zurfin kilomita 10, inda ta lalata yankin Ahar a ranar Asabar da misalin karfe hudu da mintoci 53 na yamma agogon wurin. Kuma an samu wata girgizar kasa ta biyu mai karfin 6 bisa ma'aunin Richter da ta abku bisa zurfin kilomita 10 a yankunan Varzaqan da misalin karfe biyar da mintoci hudu na yamma agogon wurin, a cewar cibiyar kula da girgizar kasa ta kasar Iran.

"MDD a shirye take wajen bada taimakon jin kai da ake bukata game da irin wannan bala'i, haka kuma za ta nemi taimako daga kasa da kasa kan wannan lamari," sanarwar ta kara jaddadawa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China