in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane kimani 170 suka mutu ko raunana sakamakon rikicin da ya abku tsakanin Isra'ila da Palasdinu
2011-05-16 10:09:58 cri

Ranar Lahadi 15 ga wata, rana ce ta tunawa da masifar Palasdinu, a wannan rana, dubban Palasdinawa masu zanga-zanga sun tada rikici da sojojin Isra'ila a zirin Gaza, kudancin Lebanon yankin Golan na kasar Sham, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 10 yayin da wasu 160 suka raunana.

Darurukan fararen hula na zirin Gaza sun taru suka yi zanga-zanga a wani tashar bincike ta kasar Isra'ila dake arewacin zirin Gaza domin tunawa da ranar masifa ta 63. Yayin da matasa fiye da goma sdake dab da tashar, aka harbe su, mutum 1 ya mutu yayin da wasu 60 suka raunana, kuma 3 daga cikinsu sun ji mumunan rauni.

A wannan rana kuma, dubban Palasdinawa dake zaune a kasar Lebanon sun taru suka yi zanga-zanga a wani yanki dake kan iyaka tsakanin Lebanon da Isra'ila domin tunawa da ranar. Wasu Palasdinawa da suka nufin shingen iyakar, sojojin Isra'ila sun yi harbi sama domin yin gargadi, amma wasu Palasdinawa sun daga tuta suna jifin wadannan sojojin da duwatsu, daga baya, sojojin suka harbe su, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 yayin da wasu 56 suka raunana.

Baya da wannan kuma, a wannan rana, masu zanga-zanga na kasar Sham da suka dab da yankin iyaka na soja na kasashen Isra'ila da Sham dake yankin Golan, sun tada rikici da sojojin Isra'ila, sojojin sun harbe wadanda suke kokarin ketare yankin, mutane 4 sun mutu, yayin da wasu 40 suka raunana.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China