A wannan rana kuma, babban taron ya yi wani zama mai jigon "Samun bunkasuwa mai dorewa da sauyin yanayi". Vuk Jeremić ya yi jawabi a gun taron inda ya ce, wani babban kalubale da ake fuskanta a wannan zamani shi ne kawar da talauci da rage gibin dake tsakanin matalauta da masu arziki a duniya ba tare da barnata muhallin zaman rayuwar dan Adam ba.
Ya ce, tsarin da ake bi yanzu na samun bunkasuwa zai haifar da masifa a duniya, don haka ya yi kira da a rage dogaro da makamashi dake fitar da hayaki na carbon-dioxide, ta yadda za a kiyaye muhallin duniya bisa halin da ake ciki na samun matsalar sauyin yanayi mai tsanani.
Vuk Jeremić ya kuma jaddada cewa, ana bukatar kasa da kasa su kafa dangantakar abokantaka bisa hanyar da ake bi domin samun bunkasuwa mai dorewa, inda ya ce bai kamata a bar wata kasa a baya ba, ko kuma ya kasance wata kasa ba ta shiga wannan aiki ba. Dadin dadawa, ya yi kira ga kasashe daban-daban su yi hadin kai domin gabatar da wani sabon shiri kan wannan batu. (Amina)