A yammacin ranar 4 ga wata ne, a birnin Doha hadkwatar kasar Qatar, aka kaddamar da babban taro kan batun kare gurbatar yanayi na MDD, manyan jami'ai daga kasashe da yankuna kimanin 200 ne suka halarci bikin.
Yayin jawabinsa a wajen taron, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya ce, ya kamata, dukkanin al'ummun duniya su shiga tinkarar barazanar da sauyin yanayi ke kawowa. Ban da haka, ya shawarci kasashe da suka kulla yarjejeniya da su ba da damar daukar matakai yadda ya kamata yayin da ake ci gaba da gudanar da taron, domin tabbatar da muhimman abubuwa biyar, ciki har da zartas da wa'adi na biyu na yarjejeniyar da za a amince da ita, da samun jari cikin dogon lokaci, da kuma ba da tabbaci ga aiwatar da wasu hukumomi wadanda suke taimakawa kasashe masu tasowa wajen rage fitar da gurbatacciyar iska mai dumama yanayi yadda ya kamata, ciki har da asusun GCF da sauransu, haka nan akwai batun daukar matakin da ya dace, wajen rage gibin dake tsakanin hakikkanin halin da ake ciki da hasashen da ake yi na gaba. (Amina)