Baya da haka kuma, Xie Zhenhua ya gabatar da ra'ayoyi hudu dangane da babban taron Doha, wato tsayawa tsayin daka kan bin tsare-tsare, da daukar babban nauyi a kokarin tabbatar da yarjejeniyar Bali, da cika alkawali a kokarin karfafa hadin gwiwa da amincewa da juna, da kuma samar da makoma mai kyau ta hanyar aiwatar da yarjejeniya yadda ya kamata.
A wannan rana kuma, an gudanar da dandalin tattaunawa kan cinikayyar carbon da bunkasa tattalin arziki mai tsimin makamashi na kasar Sin a rumfar kasar Sin a wannan taro na kasar Qatar, inda Xie Zhenhua ya gabatar da yanayin da ake ciki a kasuwannin carbon na Sin. Ya ce, za a yi kokari sosai wajen cimma burin yin tsimin makamashi da rage fitar da yawan gurbatacciyar iska. A kokarin cimma wannan buri, kuma a lokaci shirin samun ci gaba na tsawon shekaru 5 na 11, kasar Sin ta riga ta zuba jari sama da yuan biliyan 1000 a wannan fanni. Idan kuma ana fatan cimma shirin na 12 na shekaru 5, za a zuba jari sama da yuan biliyan 2000, yayin da zaman al'ummar kasar zai zuba kudi sama da yuan biliyan 4000. A sabili da haka, dole ne mu yi kokarin cimma burin, tare da rage yawan kudin da za a kashe. Shi ya sa mun yi amfani da wannan tsari na cinikayyar carbon.(Fatima)