Dalili shi ne wasu kasashe masu ci gaba sun ki ba da hadin kai, don haka aka kasa samun cigaba a cikin shawarwari, wato kan aikin mataki na biyu na "yarjejeniyar Kyoto", shirye-shiryen "dandalin Durban", da dai sauran muhimman batutuwa ba.
Yanzu dai za a tattauna duk wadannan batutuwa a yayin shawarwarin mataki na biyu. Daga ranar 3 ga wata zuwa ta 7, taron yanayin Doha zai shiga mataki na biyu, watau, matakin shawarwarin matsayin koli. Ana tsammani cewa, mai yiwuwa ne, za a samu kyakkyawan sakamako a yayin wannan lokaci.
Masu yin nazari suna hasashen cewa, kasashe masu ci gaba ba za su nuna hadin kai cikin sauki ba kan batun rage yawan iska mai gurbata muhalli da kuma wajen ba da taimakon kudi, shi ya sa, mai yiyuwa ne za a kara kwanakin taron yanayin Doha. Bugu da kari, kila ne ba za a iya samun cigaba ko kadan ba bisa dalilin son kai da kuma taurin kai na kasashe masu cigaba. (Maryam)