Kungiyar WMO ta furta cewa, tun bayan shekarar 1971, an fara samun dumamar yanayi a duniya a bayyane, zafin da ke karuwa da digri 0.166 kan ma'aunin selsus a shekaru goma-goma.
Babban sakataren kungiyar, Michel Jarruad ya bayyana cewa, ko da yake karuwar zafin a duniya a sakamakon ayyukan bil adam ba za ta yi barazana ba, amma lallai tana kasancewa. Sauyawar yanayi za ta kawo babbar illa ga doron duniya, iska, teku da sauransu ba tare da samun kyautatuwa ba.(Fatima)