A cewar Christiana Figuere, sakatriyar zartaswa ta hukuma mai kula da yarjejeniyar shawo kan matsalar sauyin yanayi ta MDD, burin da ake neman cimmawa a wannan taro shi ne tsawaita wa'adin yarjejeniyar Kyoto, da kiyaye wani tsari na bin yarjeniyoyi 2 wajen kokarin tinkarar sauyawar yanayi.
A nasu bangare, Kasar Sin, India, Brazil da Afirka ta Kudu, wadanda ke halartar taron COP17/CMP7 a matsayin wakilan kasashe dake tasowa, sun jaddada cewa, yarjejeniyar Kyoto ta kasance tushe na shawarwarin MDD kan batun sauyin yanayi, kana ya kamata a ba da fifiko ga aikin tabbatar da wa'adi na 2 na yarjejeniyar don ci gaba da kokarin cika alkawarin da aka dauka.
Wa'adin farko na yarjejeniyar Kyoto, wadda aka kulla a shekarar 1997, zai cika a shekarar 2012. Sakamakon yadda wasu kasashe masu sukuni suka ki amincewa da wa'adi na 2 na yarjejeniyar, shi ya sa ake sanya ayar tambaya kan shin ko za a iya tsawaita wa'adi na yarjejeniyar. (Bello Wang)