in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gabatar da takardar tinkarar sauyin yanayi ta shekarar 2011
2011-11-22 14:57:42 cri

Yau Talata 22 ga wata, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gabatar da takardar manufofi da ayyukan da Sin ta tsara wajen tinkarar sauyin yanayi a shekarar 2011, inda ta yi cikakkun bayanai kan manufofi da ayyukan da Sin ta tsara wajen tinkarar sauyin yanayi da ci gaba da ta samu tare da tsare-tsare da matsayin da Sin ta dauka kan wannan batu daga shekarar 2011 zuwa ta 2015.

Takardar ta nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta mai da aikin kokarin tinkarar sauyin yanayi a matsayin wani babban batun bunkasa tattalin arziki da al'ummar kasar Sin, kuma ta shigar da shi cikin babban tsari na matsakaici da dogon lokaci na bunkasa tattalin arziki da al'ummar kasar Sin.

Takardar ta ce, Sin ta sauke nauyinta wajen kokarin yin shawarwari da kasa da kasa kan batun sauyin yanayi da kara yin musayar ra'ayi da kasa da kasa kan wannan batu a fannoni daban-daban, tare da kokarin sa kaimi ga bangarori daban-daban da su cimma matsaya daya kan lamarin. Baya da wannan kuma, Sin ta yi kokarin yin hadin kai tsakaninta da gwamnatoci daban-daban, kungiyoyi da hukumomi kasa da kasa bisa ka'idar kawo moriyar juna, samun ci gaba mai kyau domin sa kaimi ga al'ummar duniya da ta samu ci gaba mai kyau a fannin tinkarar sauyin yanayi.

Hakazalika, takardar ta ce, daga karshen watan Nuwamba zuwa farkon watan Disamba na bana, za a kira taron tattaunawa kan batun sauyin yanayi na MDD a birnin Durban na kasar Afrika ta kudu. A ganin kasar Sin, kamata ya yi, taron ya tabbatar da yarjejeniyar da aka sa hannu a taron Cancun na shekarar 2010 tare da ci gaba da yin shawarwari kan wasu batutuwa da ba a cimma matsaya a kansu ba a taron Cancun.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China