in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude babban taron canjin yanayi na duniya a birnin Doha.
2012-11-26 20:07:00 cri
An bude babban taro na duniya game da canjin yanayi a yau Litinin 26 ga wata a birnin Doha na kasar Qatar, inda wakilai daga kasashe fiye da 190 suka hallara domin tattauna manyan batutuwan da suka shafi abubuwan hana dumamar yanayi da suka hada da cikakkaun bayanai dake kunshe a cikin yarjejeniyar Kyoto.

Mahalarta taron da aka ma lakani da " Taron jam'iyyu 18" na tsarin da MDD ta shirya game da canjin yanayi, ana sa ran za su matsa lamba na ganin a cimma batutuwan da aka amince da yinsu a taron shekarun baya don samar da ingantaccen sakamako.

A lokacin bikin bude taron, shugaban karba karba na taron na 17 mai barin gado wanda ya fito daga kasar Afrika ta Kudu Maite Nkoana-Mashabane ya sanar da mika ragamar jagorancin taron na wannan karon ga Abdullah bin Hamad Al-Attiyah, shugaban cibiyar mulki da inganta ayyuka a bayyane ta kasar Qatar,.wanda shi kuma sabon shugaban a cikin jawabinsa na karbar ragamar jagoranci ya ce, canjin yanayi wani babban kalubale ne dake fuskantar al'ummomin duniya, don haka ya kamata a aiwatar da ayyukan da za'a iya tinkararsu.

Ya kara da cewa, wannan taron da zai dauki tsawon makwanni biyu yana da matukar muhimmanci ga ko wane mahalarcin taron domin inganta fasaharsa, ta yadda za'a taimaka wajen rage dumamar yanayi.

A nata jawabin, babbar sakatariya ta hukumar kula da canjin yanayi ta duniya dake karkashin MDD Christiana Figueres a wajen taron ta ce, tattaunawar da za'a yi a Doha za ta yi himma wajen ganin ya kammala ayyukan da aka fara aiwatar da su a tarukan baya musamman wanda aka fara a garin Bali na kasar Indonesiya.

Madam Figueres ta kara da cewa, abin da za'a tattauna a yanzu zai yi bayani dalla dalla game da yarjejeniyar Tokyo da kuma wani izini a shari'ance da zai sa kasashe masu manyan masana'antu su rage karfin sinadarai dake gurbata muhalli da suke amfani da su.

Haka kuma ta lurar da mahalarta taron game da bukatun karin kudade da kayayyakin da za'a samar ma kasashe masu tasowa wanda suke da matukar bukatar taimako a kokarinsu na rage dumamar yanayi. Tana mai fatan za'a samu cigaba a wannan fanni sakamakon taron na Doha.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China