Rukunin musamman da za a kafa zai kula da aikin kafa wani tsarin dokoki kafin shekarar 2015 wanda zai dace da bukatun dukkan bangarorin da suka sanya hannu kan takardun kyautata yanayin duniya. Ta haka, bangarorin za su iya tattaunawa kan yadda za su rage fitar da iska mai guba wadda kuma ka iya jawo dumamar yanayi.
Babbar jami'a mai karbar bakuncin taron ita ce minista mai kula da hulda da hadin gwiwa da kasa da kasa ta Afirka ta Kudu, Maite Nkoana-Mashabane, wadda ta ce shawarwari dangane da yanayi da aka yi a wannan karo suna da muhimmanci sosai, domin a wajen shawarwarin an tsaya kan tsarin mutunta ra'ayoyi na bangarori daban daban, da bayyana kome ba tare da rufa-rufa ba, gami da barin bangarorin da suka sanya hannu kan yarjeniyoyin kyautata yanayi su dauki nauyin ci gaban aikin, ta haka za a tabbatar da tsarin da za a bi a nan gaba wajen tinkarar sauyawar yanayi a duniya.
Xie Zhenghua, shugaban tawagar kasar Sin da ta halarci shawarwarin dangane da aikin yanayi a wannan karo, shi ma ya nuna goyon baya ga kudurin da mahalarta taron suka tsayar, inda ya ce, an samu nasarori a fannoni daban daban wajen wannan taron, ban da haka, kasar Sin za ta kara yin hadin kai da sauran kasashe masu tasowa domin kara aiwatar da wasu matakai kamar yadda aka kayyade a taron Cancun da na Durban. (Bello Wang)