logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya ce karin farashin mai da aka yi a kasar shi ne zai buda kofar cigaban kasa

2024-09-07 16:51:07 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan kasar da su kara hakuri bisa halin matsin da suke fuskanta sakamakon karin farashin man fetur da aka yi a kasar, ya ce an dauki wannan mataki mai tsauri ne a matsayin dole domin ita ce hanyar kadai da za ta bude kofofin cigaban kasa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Mr. Ajuri Ngelale ya rabawa manema labarai a birnin Abuja, ya ce shugaban ya bayyana hakan ne jiya Jumma’a 6 ga wata a birnin Beijing lokacin da ya gana da ‘yan Najeriya mazauna kasar Sin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kamar yadda sanarwa ta bayyana, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce karin farashin man fetur din da sauran sauye-sauyen tattalin arziki da yanzu haka gwamnatinsa ke yi yana daya daga cikin dabarun da za su taimakawa cigaban Najeriya cikin gaggawa.

Ya ci gaba da cewa, ya sami labarin yadda al’ummar Najeriya ke ta koke-koken a ‘yan kwanakin nan a game da karin kudin man fetur, amma wannan ba wani abu ba ne da zai dore, ba da jimawa za a fara ganin fa’idarsa sosai ga yanayin rayuwa da cigaba a dukkan fannoni.

Shugaba Tinubu haka kuma ya shaidawa ‘yan Najeriyar dake zaune a kasar China cewa, muna son Najeriya ta kasance kamar kasar Sin ta fuskar ingantattun hanyoyin mota, da ruwan sha tsaftacce da wadataccen wutar lantarki sannan yaranmu su samu ilimi mai inganci.

Ya ce babu yadda za mu yi mu kai ga wannan matsayi ba tare da mun dauki wannan mataki mai tsauri ba, inda ya kara da cewa Najeriya tana da hazikan mutane masu fikira da karfin hali, a don haka babu shakka nan gaba kadan za mu iya cimma burin mu. (Garba Abdullahi Bagwai)