logo

HAUSA

Yadda mata suke barci da dare da fitilu a kunne ya kan sanya su yi kiba cikin sauki

2024-09-15 18:26:40 CMG Hausa

 

Masu karatu, sanin kowa ne cewa, idan an ci abubuwa da yawa, sannan ba a motsa jiki yadda ya kamata, to, za a iya yin kiba. Amma ko kun san cewa, idan mata sun yi barci da dare, da fitilu a kunne, to, akwai yiwuwar za su iya yin kiba? Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya tunatar da mu cewa, mai yiwuwa yin barci da dare ba tare da kashi fitilu  ko kuma telibijin ba, zai kara wa mata kiba.

An kaddamar da wannan sakamakon nazari a cikin mujjalar kungiyar ilmin likitanci ta Amurka wato The Journal of the American Medical Association, inda aka yi karin bayani kan alakar da ke tsakanin hasken fitilu da kiba.

Masu nazari daga kwalejin nazarin lafiya na kasar Amurka sun baiwa mata dubu 43 da 722 wadanda shekarunsu suka wuce 35 amma ba su kai 75 a duniya ba takardar tambayoyi dangane da ko suna yin aikin dare ko a’a, ko sun samu ciki ko a’a, ko sun taba kamuwa da ciwon sankara ko ciwon magudanar jini a zuciya ko a’a. Ban da wannan kuma, wadannan mata sun rubuta ko sun yi barci ba tare da kashe fitilu a cikin daki ko a’a, ko akwai hasken fitilu a wajen dakinsu ko a’a, ko suna barci ba tare da kashe telibijin ba ko a’a. A karshen takardar binciken, sun rubuta nauyin jikinsu, tsayinsu, awon kunkumi da girman tuwon duwawu da mizanin BMI na awon nauyin mutum.

Bayan da masu nazari sun kwatanta bayanan da suka samu da bayanan lafiyar wadannan mata bayan shekaru 5, sun gano cewa, idan akwai hasken fitilu ko kuma an bude telibijin yayin da suke barci da dare, to, yiwuwar karuwar fiye da kilo 5 na nauyin jikinsu ta karu da kashi 17 cikin kashi 100. Idan akwai hasken rana a wajen dakin da suke barci da dare, to, kusan babu wata alaka a tsakanin lamarin da kuma karuwar nauyin jikinsu.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, mu ‘yan Adam muna daukar shekara da shekaru muna samun ci gaba. Yanzu mun saba da haske da rana, da kuma dare. Idan akwai hasken fitilu ko hasken telibijin da dare, to, hakan na iya sauya yawan kwayoyin halittar jinsi da ke jikin dan Adam(Hormone), da kuma yadda suke rayuwa, ta yadda hakan zai iya kara barazanar yin kiba da sauran matsalolin lafiya. (Tasallah Yuan)