logo

HAUSA

Faransa: Mahaifa mata sabbin hannu na fama da cutar damuwa

2024-08-13 15:34:27 CMG Hausa

 

Masu nazari na kasar Faransa sun kaddamar da sakamakon nazari a kwanan baya cewa, binciken da aka gudanar dangane da tunanin mata masu jego a kasar ya nuna cewa, wasu kashi 16.7 cikin kashi 100 daga cikinsu na fama da cutar damuwa bayan haihuwa, yayin da wasu fiye da rubu’i su kan damu a kullum.

Tawagar nazari karkashin sashen kula da lafiyar tunani na hukumar kiwon lafiyar kasar Faransa ta tantance bayanan da suka shafi lokacin goyon ciki, wato daga makonni 28 na samun ciki zuwa mako 1 bayan haihuwa. A kan tattara irin wadannan bayanai sau daya a ko wadanne shekaru 5 zuwa 6 tsakanin wasu matan da suka haihu a mako guda a kasar Faransa. An samu sabbin alkaluma ne a watan Maris na shekarar 2021, inda masu jego suka amsa tambayoyin da aka yi musu dangane da lafiyar tunani. A karo na farko, hukumar kiwon lafiya ta Faransa ta kimanta yanayin tunanin masu jego cikin makonni 2 bayan sun haihu bisa wadannan alkaluma.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, wasu masu amsa tambayoyin da yawansu ya kai kusan kashi 30 cikin kashi 100 sun nuna cewa, sun yi fama da matukar gajiya, saurin fushi, damuwa mai wuyar raguwa cikin watanni 2 bayan sun haihu. Kana kuma, yawan masu kamuwa da cutar damuwa bayan haihuwa ya kai kashi 16.7 cikin kashi 100 bisa jimillar dukkan masu amsa tambayoyin. Ban da haka kuma, wasu wadanda yawansu ya kai kashi 27.6 cikin kashi 100 sun taba nuna damuwa kan wasu al’amura.

Hukumar kiwon lafiya ta kasar Faransa ta yi nuni da cewa, alkaluman da suka samu daga nazarinsu sun yi daidai da alkaluman da aka samu a kasashen duniya, wato yawan masu jego da suka kamu da cutar ta damuwa bayan haihuwa ya kai kashi 10 zuwa 20 cikin kashi 100 bisa jimillar mahaifa mata.

Ta yaya za mu taimakawa masu jego? Madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ba da shawarar cewa, akwai dalilai da dama da suke sanya mahaifa mata su kamu da cutar damuwa bayan haihuwa. Bai kamata mu kaskantar da cutar da illolin da cutar ke haifarwa da kuma alamu masu ruwa da tsaki ba. Ya zama tilas abokan zaman masu jego, iyalansu da abokan aikinsu su lura cewa, mata da yawa suna fama da matsalar tunani bayan haihuwa, ta haka za su iya taimaka musu.