logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken
Rediyo
  • In Ba Ku Ba Gida
  • Sin da Afirka
  • Duniya A Yau
  • Wasannin Motsa Jiki
  • Allah Daya Gari Bambam
  • Liang Jianying, injiniya ce da ta jagoranci kera jiragen kasa a yayin da take da shekaru 23, da jiragen kasa masu sauri a yayin da take da shekaru 34

    Liang Jianying tana da alaka da jiragen kasa tun tana karama, kuma ta zama mai tsara layin dogo bayan kammala karatunta a jami'a. Ta jagoranci tawagarta wajen samun manyan fasahohin zamani, da samar da nau’ikan jiragen kasa masu sauri daban-daban, tare da taimakawa aikin gina layin dogo na kasar Sin wajen samun ci gaba cikin sauri. Har ma ta lashe lambar yabo ta "Injiniya ta kasa" a kasar Sin, kuma ta zama jarumar da ta cancanci yabo a fannin aikin gina layin dogo.

  • Sin da kasashen Afirka na kokarin inganta hadin gwiwar kwararru a fannoni daban daban

    A shekarun nan, a karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC a takaice, hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na kara zurfi a fannin horar da kwararru. A cikin shirinmu na yau, bari mu je wurin samar da horon sana’o’i na Luban dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, da kwalejin Confucius ta jami’ar Dar es Salaam dake kasar Tanzaniya, don ganin nasarorin da aka samu ta hanyar hadin gwiwar kwararru tsakanin Sin da kasashen Afirka.

  • Ana fatan baje koli na Canton Fair zai samu sabon ci gaba a sabon zamani

    An bude baje kolin hajojin da ake shigowa, gami da wadanda ake fitarwa zuwa ketare na kasar Sin wato “Canton Fair” a tsakiyar watan nan na Afirilu, bikin da ya zamo karo na 135. An fara gudanar da shi ne tun daga lokacin bazarar shekara ta 1957, kuma ake ci gaba da yin sa sau biyu a kowace shekara a birnin Guangzhou, na larding Guangdong, wato a lokutan bazara da na kaka.

  • Wacce Kungiya Ce Za Ta Iya Lashe Gasar Firimiya?

    Kawo yanzu dai saura wasanni bakwai a kammala gasar Firimiya ta Ingila kuma za a iya cewa kungiyoyi uku ne a cikin kungiyoyi 20 za su iya lashe gasar ta bana da suka hada da Manchester City, wadda ta lashe gasar a kakar da ta gabata da Liberpool da kuma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal wadda rabon ta da lashe gasar yau shekara 20 kenan.

  • Cikakken tsarin masana'antu na taimakon kirkirar sabbin fasahohi a Sin

    A cikin shirinmu na yau, za mu duba yadda kasar Sin take yin amfani da cikakken tsarinta ta fuskar masana'antu wajen raya sabbin fasahohin da ake bukata.

LEADERSHIP