logo

HAUSA

Raunin mata a lokacin yarantaka kila zai kara musu hadarin kamuwa da cututtukan biyon bayan samun ciki

2024-07-15 19:55:54 CMG Hausa

 

Masu nazari daga jami’ar Queensland ta kasar Australiya sun kaddamar da wani sakamakon nazari a ‘yan kwanakin baya cewa, idan an ci zarafin mata, ko kau da kai daga wajensu ko kuma an muzguna su a gida a lokacin da suke kanana, to, watakila matan za su kara samun hadarin kamuwa da cututtukan da su kan biyo bayan samun ciki ko haihuwa kafin lokaci.

Da ma sakamakon nazari ya shaida cewa, raunin da aka samu a lokacin yarantaka kan yi illa ga lafiyarsu a lokacin da suka balaga, amma ba a tabbatar da cewa, hakan zai ci gaba har bayan sun samu ciki ba. Masu nazari daga jami’ar Queensland sun tantance bayanan da aka tanada cikin rahotannin nazari guda 21 da aka kaddamar tsakanin shekarar 1994 zuwa ta 2022, sun kuma gano cewa, idan an ci zarafin kananan yara mata, ko kau da kai daga gare su, ko ba a kula da su ba, ko kuma an muzguna su a gida, to, yiwuwar kamuwa da cututtukan da su kan biyo bayan samun ciki da suke fuskanta bayan sun balaga, ta fi wadanda ba a yi musu hakan ba yawa har da kashi 37 cikin kashi 100, kana kuma yiwuwar da suke fuskanta ta haihuwar jarirai sirara ko haihuwa kafin lokaci ta fi yawa har da kashi 31 cikin kashi 100. Matan da aka gudanar da nazarin kansu, mata ne da suka fito daga kasar Amurka, Canada da kasashen Turai.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, watakila raunin da aka samu a lokacin yarantaka, zai illata yadda mutane suke shawo kan damuwa da kuma garkuwar jiki, da sauya tsarin kwakwalwa da amfaninta, da sanya kwayoyin halitta su tsufa cikin sauri, lamarin da zai sanya mata su kara fuskantar hadarin kamuwa da cututtukan da su kan biyo bayan samun ciki.

Har ila yau, masu nazarin sun yi nuni da cewa, sun gudanar da nazarin kan matan da suka fito daga kasashen yammacin duniya masu yawan kudin shiga. Don haka ba su iya kimanta halin da ake ciki a sauran yankunan duniya da kuma boyayyun illolin da mabambantan rauni sukan yi wa lafiyar mutane ba. Duk da haka kulawa da masu juna biyu wadanda suka ji rauni a lokacin da suke kanana bisa bukatunsu, zai taimaka wajen kyautata lafiyar jiki da ma tunani mata masu juna biyu da jariransu.(Tasallah Yuan)