logo

HAUSA

Nazari: Salon rayuwa mai inganci na iya magance shiga damuwa

2024-08-19 19:33:50 CMG Hausa

 

Bayanai na nuna cewa, kula da salon rayuwa yana da alaka da lafiyar jiki na dogon lokaci, kuma bincike na baya-bayan nan ya tabbatar da cewa, kuma haka batun yake ga lafiyar kwakwalwa.

Sakamakon bincike na baya-bayan da aka wallafa a mujallar kula da lafiyar kwakwalwa, da ake kira “Nature Mental Health”, ya nuna cewa, abubuwa bakwai dake shafar salon rayuwa, da suka hada da, matsakaicin shan barasa, da cin abinci mai kyau, da motsa jiki na yau da kullun, da samun isasshen barci, da kaurace wa shan taba sigari, rage yawan zama a wuri guda da yin mu’amula da jama’a, suna da alaka da rage shiga damuwa.

Tawagar masu bincike na kasa da kasa daga cibiyoyi da dama da suka hada da jami'ar Fudan ta kasar Sin da jami'ar Cambridge da ke kasar Birtaniya ne suka gudanar da shi cikin hadin gwiwa.

Tawagar ta gano abubuwa guda 7 dake shafar salon rayuwa mai kyau, ta hanyar nazarin bayanan da aka tattara daga kusan mutane dubu 290 daga UK Biobank, wato babban rumbun bayanan nazarin halittu da albarkatun bincike na Birtaniya.

Sakamakon binciken da aka gudanar ya nuna cewa, daga cikin wadannan abubuwa guda bakwai, samun barci na tsawon sa'o'i 7 zuwa 9 a dare, yana da matukar tasiri, domin yana rage hadarin kamuwa da matsalar damuwa da kashi 22 cikin kashi 100. Sai kuma kauracewa shan taba sigari, wanda ke rage hadarin da kashi 20 cikin kashi 100. Kiyaye mu’amula da jama’a, yana rage hadarin da kashi 18 cikin kashi 100, yin ayyukan motsa jiki na yau da kullun da kashi 14 cikin kashi 100, rage tsawon lokacin zama a wuri guda zuwa matsakaicin mataki da kashi 13 cikin kashi 100, matsakaicin shan barasa da kashi 11 cikin kashi 100, da kuma cin abinci mai kyau da kashi 6 cikin kashi 100.

Bugu da kari, binciken ya lura cewa, tsarin kwakwalwa, da na kariyar garkuwar jiki da kwayoyin halittar gado, na iya bayyana alaka tsakanin salon rayuwa da matsalar damuwa.

Baki daya, sakamakon binciken ya nuna cewa, nacewa ga tsarin rayuwa mai inganci, zai iya taimakawa wajen yin rigakafin kamuwa da matsalar damuwa. (Tasallah Yuan)