logo

HAUSA

WHO ta yi kira da a yi kokari tare don sa aya ga yaduwar cutar tarin fuka a nahiyar Afirka

2024-06-26 15:35:55 CMG Hausa

 

Wata babbar jami’ar hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO ta bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Afirka su hada hannu tare, su zuba kudi kan matakan yin rigakafi da za su yi babban tasiri, a kokarin cimma burin kawar da cutar tarin fuka a baki dayan nahiyar zuwa shekarar 2030.

Ranar 26 ga watan Maris na kowace shekara, rana ce ta yaki da cutar tarin fuka ta kasa da kasa. Madam Matshidiso Moeti, darektar hukumar WHO mai kula da harkokin Afirka ta bayyana cewa, idan gwamnatocin kasa da kasa, da ‘yan kasuwa da masu ba da tallafin kudi suka zuba kudade kan sabbin dabarun tabbatar da gano kamuwa da cutar ta tarin fuka, da samar da sabbin alluran rigakafi, da sabbin hanyoyin ba da jinya, to, akwai yuwuwar rage babban nauyin da ke wuyan kasashen Afirka wajen yaki da cutar mai hadari.

Moeti ta yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu, a nahiyar Afirka, cutar tarin fuka mai yaduwa, ita ce babban dalili na biyu dake haddasa mutuwar mutane, wadda muninta ta fi ta cutar AIDS. Ta kara da cewa, a shekarar 2022 da ta gabata, mutane kimanin miliyan 2.5 sun kamu da cutar ta tarin fuka a kasashen Afirka, wato kwatankwancin mutum 1 ya kamu da cutar a ko wadanne dakikoki 13.

A cikin sanarwar da aka bayar a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya, madam Moeti ta yi bayani da cewa, a shekarar 2022 da ta gabata, mutanen da yawansu ya kai dubu 424 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da cutar tarin fuka. Duk da cewa, ana iya rigakafi da kuma ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar, amma a kowane minti 1 wani ya rasa ransa sakamakon kamuwa da ita.

A cewar babbar jami’ar WHO, wadannan alkaluma sun tunatar mana da bukatar gaggauta daukar matakai tare don dakile yaduwar cutar ta tarin fuka a yanzu haka, tare da jaddada wajibcin ci gaba da kokarin dasa aya ga kasancewar cutar. Ta kara da cewa, sashen hukumar WHO mai kula da harkokin Afirka ya samar da jagoranci ta fuskar manyan tsare-tsare da kuma hanyoyin sa ido kan yaduwar cutar, a kokarin gaggauta takaita yaduwarta.

Babban taken ranar yaki da cutar tarin fuka a bana shi ne “E, tabbas za mu kau da cutar tarin fuka baki daya!”, a kokarin sake ilmantar da al’umma dangane da cutar, wadda gurbatar muhalli, cunkuson mutane, da talauci kan tsananta yaduwar cutar.

Madam Moeti ta yaba da gaggarumin ci gaban da Afirka ta samu wajen dakile cutar. Daga shekarar 2015 zuwa ta 2022, yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya ragu da kaso 38, kana yawan sabbin masu kamuwa da cutar a nahiyar Afirka ya ragu da kaso 23.

A cewar babbar jami’ar, yadda ake yaki da kwayoyin cutar tarin fuka masu kin jin magani, inganta sa ido, samar da isasshen kudi, yin nazari, shigar da al’umma cikin ayyuka, da kyautata tsarin lafiya, suna da matukar muhimmanci wajen kau da cutar tarin fuka daga Afirka. (Tasallah Yuan)