logo

HAUSA

Zaman mutum shi kadai na wani dan lokaci zai iya rage gajiya da damuwa

2024-08-05 16:24:49 CMG Hausa

 

A kan ce, wanda yake zamansa shi kadai kullum, mai kadaici ne. Amma fa alal hakika hakan wani nau’in rashin fahimta ne. Sakamakon wani nazari ya nuna cewa, zaman mutum shi kadai na wani dan lokaci zai iya rage masa gajiya da damuwa, kuma hakan na sanya mutane farin ciki sosai.

Masu nazari daga jami’ar Reading ta kasar Ingila, da jami’ar Tilburg ta kasar Netherlands, da jami’ar Durham ta Ingila, sun gudanar da nazari na hadin gwiwa, a kokarin tabbatar da lokaci mafi tsawo da ake iya dauka a kowace rana, wajen zaman mutum shi kadai, amma abin da suka gano ya wuce zatonsu. Sun gano cewa, idan mutane sun zauna su kadai, ba sa jin kadaici, kuma hakan na rage gajiya da damuwa da suke samu.

Masu nazarin sun gayyaci ‘yan sama da shekaru 35 a duniya mutum 178, da su rubuta harkokin yau da kullum da suke yi cikin makonni 3, dangane da tsawon lokacin zamansu su kadai a kowace rana, da hanyoyin rage damuwa, da yadda suke gamsuwa da zaman rayuwa, da gudanar da harkokin yau da kullum bisa dogaro da kai, da yadda suke jin kadaici. Ma’anar zaman mutum shi kadai ita ce rashin mu’amala da mutane fuska da fuska, kana rashin yin hira da wasu ta hanyar kafafen sada zumunta ko E-mail.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, idan wani ya tsawaita wa’adin lokacin yin zama shi kadai a rana, to, a ganinsa, damuwar da yake ji a ransa tana raguwa, kana yana kara samun damar gudanar da harkokin yau da kullum cikin ‘yanci. Amma idan ya tsawaita wa’adin lokacin zama shi kadai fiye da kima, to, zai kara jin kadaici, kuma gamsuwar sa a zaman rayuwa tana raguwa. Duk da haka, idan ya zabi ya yi zamansa shi kadai, a maimakon a tilasta masa yin hakan, to, karuwar jin kadaici, da raguwar gamsuwa da zaman rayuwa za su ragu, har su kai ga bacewa.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, sakamakon nazarinsu ya nuna cewa, mutum ya zauna shi kadai, hanya ce mai amfani ga lafiyar jiki da ma tunani. Zaman mutum shi kadai bisa son ran sa yana rage damuwar da yake ji a zaman rayuwa.(Tasallah Yuan)