logo

HAUSA

A yi gudu don yaki da cutar damuwa

2024-09-06 18:13:25 CMG Hausa

 

Baya ga kiwon lafiyar jiki, wace fa’ida mai yin gudu ke iya samu? Wani nazari da aka gudanar a kasar Netherlands ya nuna cewa, gudu na taimakawa wajen rage damuwa. Kamar yadda masu nazari suka fada, yin gudu na rage damuwa kamar an sha magani. Duk da haka, da wuya a nacewa yin gudu cikin dogon lokaci.

Masu nazari daga jami’ar “Vrije ta Amsterdam” ta Netherlands, sun gayyaci mutane 141, wadanda ke fama da cutar damuwa don shiga nazarin, inda suka bukace su da su fara gudu, ko kuma shan magani cikin makonni 16. Wasu 45 daga cikinsu sun zabi shan magani, wasu 96 kuma sun shiga kungiyar masu gudu, inda aka sa ido kansu don su yi gudu na tsawon mintuna 45 a kowane karo, kuma sau 2 zuwa 3 a kowane mako.

Baki daya, bayan makonni 16, wadannan masu aikin sa kai da yawansu ya kai kashi 44 cikin kashi 100, sun samu raguwar damuwa ko bakin ciki, musamman ma wadanda suke gudu kullum, sun fi rage damuwa da bakin ciki. Ban da haka kuma, wadanda suka fara gudu sun kyautata yanayin jikinsu. Alal misali, rage nauyin jiki, rage gwajin kunkumi, rage hawan jini, kyautata aikin zuciya. Amma yanayin jikin wadanda suke shan maganin ya lalace.

Me ya sa haka? Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta yi mana karin bayani da cewa, ana bukatar shan magani bisa lokacin da aka tsara, ba tare da sauya salon zaman rayuwa kai tsaye ba, hakan kuwa ya yi hannun riga da yadda motsa jiki kullum ke sauya bakin dayan salon rayuwar masu fama da cutar damuwa, wadanda kullum suke zaune a wani wuri cikin dogon lokaci. Wadannan mutane sun fara fita daga daki, sun tsara burikansu don cimma nasara, da kyautata jiki, da shiga harkokin al’umma.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, ko shan magani, ko kuma yin gudu suna taimakawa wajen yaki da cutar damuwa. Shan magani ba shi da hadari ga yawancin mutane. Nazarin su ya nuna cewa, mutane masu yawa suna fatan rage damuwa ko bakin ciki ta hanyar motsa jiki, amma suna gaza dagewa wajen yin gudu. A cikin nazarinsu, wasu da yawansu ya kai kashi 52 cikin kashi 100 ne daga masu gudun suka kammala shirin gudu, yayin da wasu kashi 82 cikin kashi 100 daga cikin masu shan maganin suka kammala shirinsu. Don haka, yin gudu kullum ba zai wadatar ba, sa ido da kuma karfafa gwiwa, na taimakawa wajen sabawa da motsa jiki kullum.