logo

HAUSA

Mata kan fuskanci karin barazanar kamuwa da cutar magudanar jini a zuciya idan sun gamu da matsalar kiba kafin samun ciki ko lokacin samun ciki

2024-07-08 10:11:06 CMG Hausa

Mujallar “Circulation Research” ta kasar Amurka, ta kaddamar da wani sakamakon nazari a kwanan baya, wanda ya nuna cewa, mata na iya kara fuskantar hadarin kamuwa da cututtukan magudanar jini a zuciya, idan sun gamu da matsalar kiba kafin sun samu ciki ko a lokacin samun ciki.

Kwalejin nazarin kiwon lafiya ta kasar Amurka ce ta samar da kudin tallafin gudanar da nazarin, a kokarin kara fahimtar alaka tsakanin yadda masu juna biyu suke fama da matsalar kiba da ciwon hawan jini, da matsalolin samun ciki, da kuma lafiyar magudanar jininsu a zuciya shekaru da dama bayan sun haifu.

Masu nazarin sun bibiyi mata dubu 4 da dari 2 da 16, da suka samu ciki a karo na farko, wadanda kusan rabinsu suke fama da matsalar kiba, ko kuma nauyin jikinsu ya wuce misali. An fara nazarin ne daga lokacin da suka fara samun ciki, har zuwa shekaru 3.7 bayan sun haihu. Masu nazarin sun gano cewa, a watanni 3 na farko da wadannan mata suka dauki ciki, idan sun yi fama da matsalar kiba, ko kuma nauyin jikinsu ya wuce misali, to, barazanar da suka fuskanta wajen kamuwa da ciwon sukari na lokacin samun ciki, ko kuma ciwon hawan jini na lokacin samun ciki, ta zarce ta takwarorinsu masu daidaiton nauyin jiki da har ninki 2. Haka kuma, masu juna biyun wadanda suke fama da matsalar kiba, ko nauyin jikinsu ya wuce misali, su kan fuskanci babban hadarin kamuwa da cutar magudanar jini a zuciya bayan sun haihu.

Dangane da sakamakon nazarin, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta yi mana karin bayani da cewa, idan mata sun haihu kafin lokacin da aka tsara, to, su kan fuskanci babbar barazanar kamuwa da cutar hawan jini, ciwon sukari ko matsalar yawan kitse a cikin jini ko “cholesterol” shekaru da dama bayan sun haihu.

Masu nazarin sun yi karin gaske da cewa, wasu cututtukan da suke biyo bayan samun ciki su kan kara hadarin kamuwa da cututtukan magudanar jini a zuciya kwarai da gaske. Nazarin da suka gudanar ya samar da wata shaidar kare lafiyar mata masu juna biyu, wadanda ke fama da matsalar kiba, ko kuma nauyin jikinsu da ya wuce misali.(Tasallah Yuan)