Motsa jiki da kyau na kara azama kan yin barci da kyau
2024-09-06 18:19:58 CMG Hausa
Masu karatu, ko kun taba gamuwa da matsalar barci duk da matukar gajiyar da kuka yi? Ko kun taba jin ciwo a duk jikinku bayan farkawa daga barci, kamar ba ku yi barci a dare ba? Masana ilmin likitancin motsa jiki sun yi bayani da cewa, motsa jiki ta hanyar kimiyya yana taimakawa wajen yin barci da kyau.
Gou Bo, shehun malami a sashen motsa jiki da kimiyyar kiwon lafiya na kwalejin koyon wasannin motsa jiki na Xi’an na kasar Sin ya yi bayani da cewa, sanin kowa ne cewa, wani kan dauki sulusin tsawon lokaci yana barci a duk rayuwarsa. Ko ana cikin koshin lafiya ko a’a, ya danganta da ko ana barci da kyau ko a’a. Yin barci na bai wa mutum damar kyautata jikinsa. A kan samu kuzari daga isashen barci. Motsa jiki yadda ya kamata yana iya rage matsin lambar da ake samu a duk rana, ta haka za a yi barci mai zurfi a dare.
Hakika dai a baya ba a lura da alakar da ke tsakanin motsa jiki da kuma yin barci ba, amma karin nazarce-nazarce sun gano cewa, motsa jiki yana da muhimmanci a fannonin wayar da kan jama'a game da inganta lafiya da kyautata ingancin barci.
Guo Jianjun, darektan cibiyar kirkire-kirkire ta fannin likitancin motsa jiki ta jami'ar koyar da harkokin motsa jiki ta Capital ya bayyana cewa, dalilan da suke hana a yi barci da kyau sun hada da na jiki da na tunani. Amma hanya mafi dacewa da ake bi don kyautata ingancin barci ita ce, motsa jiki yadda ya kamata. Guo ya ba da shawarar cewa, ana iya motsa jiki a lokacin aiki, alal misali, bayan daukar tsawon lokaci ana zaune kan kujere, ana iya motsa jiki. Sa’an nan a rika daukar mintoci 30 a ko wace rana ana gudu ba cikin sauri ba, ko yin iyo, ko yin rawa a babban fili da dai sauransu. Motsa jiki yana rage gajiyar da aka yi sakamakon aiki. Har ila yau kuma kafin a yi barci a dare, yin wasan Yoga da makamancin wasannin motsa jiki masu sakin jiki wadanda kuma suke amfanawa yin barci suna rage gajiyar da aka yi a duk rana, a jiki da tunani. Sakin jiki da tunani yana kara azama kan yin barci da kyau.
Duk da haka madam Zhang Chuji, wata likita dake aiki asibitin Tiantan na Beijing ta ba da nata shawarar cewa, motsa jiki fiye da yadda ake bukata ba sa amfana wa yin barci, musamman ma awoyi 2 kafin yin barci a dare, a kaucewa motsa jiki sosai. Kana kuma yin barci a makare da matasa su kan yi, ya fi yin muni ga yin barci da kyau. (Tasallah Yuan)