logo

HAUSA

Matan da su kan yi barci a makare sun fi saurin kamuwa da ciwon sukari mai nau’inⅡ

2024-07-22 10:27:34 CMG Hausa

 

Masu karatu, shin kuna kwanciya da wuri ku tashi da wuri, ko kuna barci a makare da farkawa a makare? Sakamakon nazari ya nuna mana cewa, matan da suke barci a makare da farkawa a makare, sun fi samun hadarin kamuwa da ciwon sukari mai nau’inⅡ, kana kila yawancinsu suna rayuwa ba ta hanyar da ta dace ba.

Masu nazari daga kwalejin ilmin likitanci na jami’ar Harvard ta kasar Amurka sun tantance alkaluman kididdiga dangane da lafiyar ma’aikatan jinya na Amurka, nazarin da aka gudanar kan ma’aikatan jinya kusan dubu 64 dangane da barazanar da mata ke fuskanta wajen kamuwa da cututtukan da ke addabar mutane cikin dogon lokaci. A lokacin da aka fara nazarin a shekarar 2009, shekarun wadannan ma’aikatan jinyan na tsakanin 45 zuwa 62 a duniya, kuma ba sa fama da cutar sankara, ciwon sukari da cutar magudanar jini a zuciya.

Ma’aikatan jinyan sun amsa tambayoyi dangane da lokuta. Wasu kashi 11 cikin kashi 100 kan yi barci a makare da farkawa a makare, yayin da wasu kashi 35 cikin kashi 100 ke kwanciya da wuri su tashi da wuri, sauran kuma babu lokaci da suka tsayar na barci da farkawa.

A cikin shekaru 8 daga bisani kuma, ma’aikatan jinyan sun rubuta yanayin cin abinci, sauyawar nauyin jiki, lokacin barci, al’adar shan giya da taba da motsa jiki, kamuwa da ciwon sukari tsakanin mambobin iyali da dai sauransu. Masu nazarin sun alakanta wadannan bayanai da tarihinsu na ganin likita, a kokarin tantance mutanen da suka kamu da ciwon sukari.

Masu nazarin sun gano cewa, gwargwadon wadanda suka yi barci da wuri da farkawa da wuri, matan da su kan kwanta a makare su tashi makare, sun fi samun hadarin kamuwa da ciwon sukari da kashi 72 cikin kashi 100, kana ba sa cin abinci yadda ya kamta, ba sa motsa jiki kullum, su kan sha giya da yawa, suna kuma fama da matsalar kiba.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, yin barci a makare ya kan haifar da illoli ga jikin dan Adam, lamarin da ke kara hadarin kamuwa da ciwon sukari, ciwon magudanar jini a zuciya da sauran cututtukan da ke addabar mutane cikin dogon lokaci.

Dangane da hakan, Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ba da shawarar cewa, kowa na rayuwa bisa shirin da ya tsara. Wasu suna barci da wuri, wasu kuma suna barci a makare. Zai yi wuya al’adarsu ta sauya. Amma zai fi kyau a yi kokarin yin barci da wuri.

Ta ci gaba da cewa, wajibi ne wadanda ke kwanciya a makare su kara sanin hadarin dake tattare da hakan, su rage shan giya, da dakatar da shan taba, da kara motsa jiki da samun isasshen barci, a kokarin rage barazanar kamuwa da cututtukan da ke addabar mutane cikin dogon lokaci. (Tasallah Yuan)