logo

HAUSA

An karrama tawagar likitocin kasar Sin karo na 11 a Sudan ta Kudu

2024-09-06 13:48:33 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne kasar Sudan ta Kudu da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar suka ba tawagar jami’an lafiya ta kasar Sin karo na 11 da za su bar kasar takardar shaida, tare da yabawa kyakkyawar hidimar da suka yi wa al'ummar yankunan kasa mafi karancin shekaru a duniya.

Ministan kiwon lafiya na kasar Sudan ta Kudu Yolanda Awel Deng Juach, ya bayyana cewa, tawagogin jami’an lafiya na kasar Sin sun yi tasiri sosai a fannin kiwon lafiyar kasar, ta hanyar yin musayar ilmi da fasahohin likitanci.

Ta yabawa tawagar likitocin kasar Sin karo na 11 bisa ayyukan da suka yi na ba da jinya, wanda ya amfanar da al'ummomin yankunan da ke wajen babban birnin kasar. (Mohammed Yahaya)