logo

HAUSA

Xi Jinping: Sin na maraba da kasashen Afirka da su more ci gaban bunkasuwar Sin

2024-09-05 11:06:17 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, Sin na maraba da kasashen Afirka da su more ci gaban bunkasuwar Sin, kuma ba wanda zai iya hana ci gaban tattalin arzikin Sin da Afirka. A shekarar 2022, yawan kudin cinikin da aka yi ta yanar gizo a Afirka ya kai dala biliyan 32.5. Kana an yi kiyasin cewa, wannan adadi zai kai dala biliyan 60 a shekarar 2027, yayin da yawan mutanen kasashen Afirka da za su sayi kayayyaki ta yanar gizo zai karu daga miliyan 388 a shekarar 2022 zuwa miliyan 610 a shekarar 2027. A cikin shirinmu na yau, bari mu je wajen wani bikin sayar da abubuwa da aka gayyaci jakadan kasar Ruwanda a Sin a matsayin mai tallar kaya, inda za mu ga yadda tunanin kasuwancin Sin ke ba da taimako wajen shigo da hajojin Afirka zuwa nan kasar Sin, matakin da zai tallafawa kokarin rage talauci a Afirka.(Amina Xu)