UNECA: Sin na tallafawa Afirka sauyi zuwa makamashi mai tsabta ta hanyar shigar da EV
2024-09-04 20:33:11 CMG Hausa
Mukaddashin darakta mai lura da sashen fasaha, kirkire kirkire, dunkulewa da samar da ababen more rayuwa a hukumar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ko UNECA mista Robert Tama Lisinge, ya ce kasar Sin na ingiza kuzarin da ake bukata, wajen cimma burin kasashen Afirka na sauyi zuwa makamashi maras gurbata muhalli, ta hanyar shigar da ababen hawa masu amfani da lantarki ko EVs zuwa sassan nahiyar.
Lisinge ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya, lokacin da yake karin haske game da muhimmancin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta fuskar cin gajiya daga ababen hawa masu aiki da lantarki a Afirka, matakin da ke karfafar nahiyar a bangaren sauya alkibla zuwa makamashi maras gurbata muhalli.
Jami’in ya ce nahiyar Afirka na kan turbar komawa ga tsari maras gurbata muhalli a nan gaba, yayin da kasashen ta ke rungumar ababen hawa na EVs a matsayin ginshikin hakan.
Daga nan sai Lisinge ya ce UNECA na shugabantar wannan sauyi, wanda karkashin sa hadin gwiwa da Sin zai samar da muhimmin jagoranci ga cimma burin Afirka, na sauya tafiya zuwa ga amfani da makamashi maras gurbata muhalli. (Saminu Alhassan)