logo

HAUSA

Kasashen yamma na yunkurin cimma burinsu ta hanyar goyon bayan Philiphines

2024-09-03 10:36:57 CGTN Hausa

 

A cikin kwanaki 10 da suka gabata, Philiphines ta gudanar da ayyuka 4 masu hadari a sararin teku da saman tudun ruwa na Ren’ai da Xianbin. Matakin da ya zama shaida dake bayyana laifin Philiphines a kan hadarin cin karo da jiragen ruwan kasashen biyu, kasashen yamma ba shakka suna da alaka da lamarin.

A hakika dai, ba ruwan wasu kasashen yamma, ciki har da kasar Amurka kan batun tekun kudancin Sin ba, amma sun mai da fari baki, dalilin da ya sa suke goyon bayan ayyukan takara da Philiphines ta gudanarwa, wadanda suke keta ikon mallakar cikakken yankin Sin, domin cimma burinsu.

Amma, amincewar da kasashen yamma da Amurka ke baiwa Philiphines ba za ta canja gaskiya ba, tudun ruwa na Xianbin sashi ne na kasar Sin, kuma duk wani aikin da Philiphines ta yi a wadannan wurare, ya kasance keta ikon Sin na mallakar sararin tekunta, kana ba za ta cimma nasarar mamaye tsibirori a tekun kudancin kasar Sin ba.

A halin yanzu kuma, a yayin shawarwari tsakanin Sin da Amurka bisa manyan tsare-tare a sabon zagaye, Sin ta nemi Amurka da kada ta keta ikon mallakar cikakken yankin kasar Sin bisa hujjar yarjejeniyoyin kasashen biyu, kada ta goyi bayan laifin da Philiphines ta yi. A nata bangare, Amurka ta nanata matsayinta na dakatar da nuna adawa da Sin ta hanyar karfafa kawancenta, kuma ba ta son yi sabani da kasar Sin. Amma, Amurka ta yi amai ta lashe, ta yi biris da alkawarin da ta yi a ’yan kwanakin baya kawai, ina mutuncinta? Game da EU, Sin ta shawarce ta da ta yi taka tsantsan kan lamarin, kada ta tsoma baki cikin harkokin tekun kudancin Sin. Kada ta dauki matakin da zai lalata moriyarta da mutuncinta a duniya. Sin za ta tsaya tsayin daka kan kare cikakken yankunanta da ikon mallakar sararin teku, za ta ci gaba da hadin gwiwa da sauran kasashe a wannan yanki don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin Sin. (Amina Xu)