logo

HAUSA

Sin da kasashen Afirka na tafiya kafada da kafada kan tafarkin zamanantar da kai

2024-09-03 19:02:45 CMG Hausa

A cikin shekaru 10 da suka gabata, hadin gwiwar cimma moriyar juna  tsakanin Sin da kasashen Afirka ya bunkasa zuwa matsayin inganci, inda kamfanonin Sin da dama suka aiwatar da mayan ayyukan samar da ababen more rayuwa da dama, da hadin gwiwar samar da makamashi mai tsafta a sassan Afirka, yayin da kuma albarkatun gona daga kasashen Afirka ke kara shiga cimakar kasar Sin. Wannan yanayi ya kara tabbatar da matsayar sassan biyu, ta kafa al’umma mai makomar bai daya.

Wani abun tambaya ma shi ne ko mene ne dalilin da ya sa Sin da kasashen Afirka ke kara dunkulewa waje guda ta fuskar hadin gwiwa? Ko shakka babu dalilin bai tsaya ga batun amincewa juna a tafarkin ‘yantar da kai da sassan biyu suka yiwa juna ba ne, har akwai batun burin da suke da shi na zamanantar da kai, da sauke nauyin kare moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa, tare da neman cimma daidaito, da adalci tsakanin sassan kasa da kasa.

Taron FOCAC na 2024 da ke tafe, zai haskaka sabon matsayin alakar Sin da kasashen Afirka, da ingiza sabon kuzari ga yunkurin su na zamanantar da kai.  (Saminu Alhassan)