Gwamnatin jihar Sakkwato da shugabannin addini da na al`umma a jihar sun nuna rashin goyon baya ga duk wata zanga-zanga
2024-07-27 14:44:59 CMG Hausa
Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Ahmed Aliyu ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki na jihar sun nesanta kansu da duk wata zanga- zanga da wasu ke kokarin aiwatarwa a jihar da kasa baki daya.
Ya tabbatar da hakan ne jiya Juma’a a 26 ga wata yayin babban taron masu ruwa da tsaki dake jihar wadanda suka kunshi malaman addini da shugabannin al`umma da kungiyoyin dalibai dana ma`aikata da kuma kungiyoyi masu zaman kansu wanda aka tattauna a kan halin da jihar da kuma kasa ke ciki ta fuskar tsaro da zaman lafiya.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwwai ya aiko mana da rahoto.
Gwamnan jihar ta Sokoto ya tabbatarwa jagororin zanga-zangar a jihar cewa ba za su taba samun goyon bayan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki dake jihar ba, a don haka ya shawarce su da su sauya tunani ta hanyar laluben hanyoyin mafi dacewa da za a bi domin samun saukin rayuwa a kasa baki daya.
Ya ce hakika `yan Najeriya na fuskantar wahalhalu da dama kama daga na rashin tsaro, rashin abinci da tsadar kayan abinci da sauran matsalolin kyautata rayuwa, amma duk da haka akwai bukatar al`umma su kaucewa daukar duk wani mataki da sunan neman hakki wanda zai sake nutsar da kasar cikin halin kaka-nikayi, kasancewar gwamnati na bakin kokarin warware jerin wadannan matsaloli ta hanyar managartan shirye-shirye da ta bijiro da su.
A don haka ne ma gwamnan na jihar Sokoto ya yi kira ga shugabannin da su kara zurfafa tunani domin ceto al`umma daga cikin wannan mawuyacin hali.
“Ya zama wajibi mu san cewa ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya, a don haka dole ne mu tabbatar da dorewar zaman lafiyar da hadin kan ta, wannan yunkuri na zanga-zanga babu abin da zai haifar illa koma baya tare da rusa dan cigaban da kasar ta samu a tsakanin shekara guda na jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu”(Garba Abdullahi Bagwai)