logo

HAUSA

An samar wa Kenya tallafin kudi don kau da cutar kala-azar daga kasar baki daya

2024-06-17 08:50:57 CMG Hausa

 

Kungiyoyin jin kai na kiwon lafiya ta kasa da kasa wato LifeArc da FIND sun sanar a kwanan baya da cewa, za su samar wa kasar Kenya da ke gabashin nahiyar Afirka tallafin kudi da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 7.8 wajen goyon bayan kokarin da kasar take yi na kau da cutar kala-azar daga kasar baki daya.

To, mene ne cutar kala-azar? Madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, cutar ta kala-azar, wani nau’in cuta ne mai hadari matuka da kwarin Sandfly suke bazawa tsakanin mutane, musamman ma tsakanin kananan yara.

A cikin wata sanarwar da wadannan kungiyoyin 2 suka bayar a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya, sun bayyana cewa, sabon tallafin kudin zai kyautata yadda ake tabbatar da gano kamuwar cutar kala-azar tsakanin yara da kuma ba su jinya yadda ya kamata.

Mike Strange, babban jami’in kungiyar jin kai ta LifeArc mai kula da harkokin kiwon lafiyar al’ummar kasa da kasa ya jaddada muhimmiyar rawar da tallafin kudi da abokan hulda suke takawa a fannin kara azama kan kau da cutar ta kala-azar baki daya. Cutar kala-azar tana yaduwa a yankunan karkara a kasar Kenya.

Mista Strange ya kara da cewa, yin hadin gwiwa da kungiyar jin kai ta FIND wajen goyon bayan daukar matakan da ke akwai a yanzu da kuma taimakawa kaddamar da sabbin dabarun tabbatar da gano kamuwa da cutar da kyautata tsoffin dabarun, wata kyakkyawar dama ce da za ta kai ga samun sauyi sannu a hankali, ta yadda a karshe za a kai ga kau da mummunar cutar kala-azar mai yaduwa daga kasar Kenya baki daya.

Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa ta WHO ta tsara manufar kau da cutar ta kala-azar baki daya ya zuwa shekarar 2030, wadda kwarin Sandfly ke yadawa tsakanin mutane, musamman ma kananan yara a yankunan karkara masu kazanta a nahiyar Afirka. Cutar ta kala-azar kan yi sanadin mutuwar mutanen da yawansu ya zarce kashi 95 cikin kashi 100, idan aka jinkirta jinyarta.  

Ban da haka kuma, wadanda suke fama da cutar kan fuskanci matsalar raguwar nauyin jiki, da kumburin saifa da hanta.

Ana sa ran cewa, sabon tallafin kudin zai kyautata ilmantar da al’ummar kasar Kenya dangane da cutar, da inganta kayyayakin kiwon lafiya a wurin, ta yadda za a kara saurin tabbatar da gano kamuwa da cutar ta kala-azar da ba da jinya yadda ya kamata.

Kamar yadda Helen Bokea, darektar kungiyar FIND mai kula da cututtuka masu yaduwa ta fada, inganta sa ido, yin bincike da ba da jinya, suna da matukar muhimmanci wajen kai ga kau da cutar daga Kenya baki daya, zuwa shekarar 2030. (Tasallah Yuan)