logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da ministar wajen Japan

2024-07-26 19:40:13 CMG Hausa

Yau Jumma’a, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma ministan harkokin wajen Sin, Wang Yi, ya gana da ministar harkokin wajen kasar Japan, Yoko Kamikawa a birnin Vientiane, babban birnin Laos.

Wang Yi ya bayyana cewa, dangantakar Sin da Japan tana cikin matsayin muhimmanci, idan ba ta ci gaba ba, to za ta koma baya. Manufar Sin game da Japan ta kasance ta kwanciyar hankali da dadewa, ana fatan bangaren Japan yana dauke da kyakkyawar ra’ayi game da Sin, da kuma gudanar da manufofi masu amfani ga Sin.

Yoko Kamikawa ta ce, bangaren Japan na tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak, wanda ba zai canza ba ko kadan. A gaban kalubalolin rikicin kasa da kasa da yankuna, bangaren Japan yana so ya inganta kwanciyar hankali da wadata na yankuna tare da bangaren Sin.

A ran nan, Wang Yi ya kuma gana da sakataren harkokin waje da raya kasa na Birtaniya, David Lammy, da ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu Cho Tae-yul, da babban wakilin EU kan harkokin waje da manufofin tsaro Josep Borrell Fontelles, da kuma sakataren harkokin wajen Norway Espen Barth Eide.(Safiyah Ma)