logo

HAUSA

Sin ta dukufa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya

2024-07-25 19:59:50 CMG Hausa

Yau Alhamis, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta shirya taron manema labarai na yau da kullum.

Dangane da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, Mao Ning ta ce, kasar Sin a ko da yaushe tana himmatuwa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, da sa kaimi ga ci gaba da wadata, kuma za ta ci gaba da tallafawa kasashen yankin Gabas ta Tsakiya wajen karfafa 'yancin kai na manyan tsare-tsare, da hadin kai, da kuma magance matsalolin tsaro na yankin.

Game da dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Brazil, Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninta da Brazil, kana tana maraba da Brazil da ta shiga cikin shawarar ziri daya da hanya daya da sauri.

Dangane da ziyarar da firaministar Italiya za ta kai kasar Sin a baya-bayan nan, Mao Ning ta ce, kasar Sin na son yin amfani da wannan ziyara a matsayin wata dama ta zurfafa hadin gwiwa mai amfani na bangarorin biyu.(Safiyah Ma)